Al'uma ta fara kaɗa ƙuri'a a zaɓen gama gari a Nijar
January 31, 2011A wannan Litinin al'uma a Jamhuriyar Nijar ke kaɗa ƙuri'a a zaɓuɓɓukan shugaban ƙasa da na 'yan majalisun dokoki zagaye na farko. Zaɓen wanda ake sa ran sama da mutane miliyin shidda ne waɗanda aka yi wa rajista za su jefa ƙuri'a na da nufin mayar da ƙasar bisa tafarkin dimokuraɗiyya bayan juyin mulkin da sojoji suka yi, yau kusan shekara guda kenan, wanda ya hamɓarar da gwamnatin Tanja Mamadou wanda ya ci gaba da yin mulki har bayan ƙarshen wa'adinsa na mulki.
'Yan takara guda guda goma ne dai za su fafata a zaɓen wanda ya haɗa da tsofon firaminista na tsofuwar gwamnatin Tanja Mamadou, Seyni Omar shugaban jam'iyar MNSD Nasara da tsofon shugaban ƙasar Mahaman Ousman da kuma tsofon firaminista Hama Amadou. Ana hasashen cewa dai in dai har ba wanda ya samu sama da kashi 50 cikin ɗari na ƙuri'un a zagayen na farko to dole ne sai an kai ga yin zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasar. Tuni dai da wasu 'yan takara shidda suka yi ƙawance domin marama ɗaya daga cikinsu baya a zagaye na biyu domin ƙalubalantar takarar jagoran 'yan adawa Mahamadou Issoufou shugaban jam'iyar PNDS Tarayya.
Wakilin DW a birnin Yamai ya shaida mana cewa tuni dai shugaban gwamnatin Jamhuriyar ta Nijar janar Salou Djibo tare da wasu membobin gwamnatinsa suka kaɗa ƙuri'a a mazaɓa ta farko mai lamba 001.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita: Mohammad Nasiru Awal