Allura ta tono garma a jarabawar JAMB a Najeriya
May 15, 2025Hukumar kula da shirya jarabawar shiga jami'o'i da manyan makarantu ta Najeriya JAMB ta bayar da kai bori ya hau bayan matsin lamba da ya tilasta bitar daukacin jarabawar ta UTME da aka yi saboda mummunar faduwar da daliban suka yi, inda aka gano kwamacalar da aka tafka bisa kuskuren na'urarorin da aka yi amfani da su. An gano cewa akwai inda tambayoyi ne kawai aka gani amma babu amsoshin da dalibai za su zaba musamman a darasin lissafi, abin da ya sanya shugaban hukumar Farfesa Ishaq Oloyede, kaiwa ga fashewa da kuka a lokacin da ya dauki nauyin laifin tare kuma da rokon gafara.
Karin bayani: Najeriya: Mecece makomar karatun jami'a?
Farfesa Oloyede ya ce: ‘'A matsayina na shugaban hukumar shirya jarabawar shiga jami'o'i da manyan makarantu ta JAMB, na dauki laifin sakacin da masu samar mana da na'urorin shirya jarabawar suka yi. Ina mai bayar da hakuri saboda halin tashin hakali da damuwa da wannan ya jefa wadanda abin ya shafa. Ina mai bayar da tabbacin cewa wannan al'amari ya haifar da komabaya. Dabi'armu ce mu amince mun yi kuskure don mu 'yan Adam ne, ba za mu ce mun iya komai ba''.
Korafin iyayen daliban da suka yi jarabawar JAMB
Iyayen yara sun harzuka saboda faduwar jarabawar da aka dade ba'a ga irinta ba da 'ya'yansu suka yi, abin da ya sanya korafe-korafensu na neman a sabunta jarabawar a fadin Najeriya, kamar yadda Idris Damjuma Abdullahi, mahaifin yara biyu suka rubuta jarabawar JAMB ya bayyana. Sai dai hukumar ta amince da sake jarabawar ne a cibiyoyi 157 da aka fi samun wannan matsala. Amma Dr Kabir Danladi Lawanti, malamin makaranta a Najeriya ya bayyana cewar akwai wasu karin matakai da hukumar JAMB za ta iya dauka.
Tun da aka nada shi a shugabancin wannan hukuma ta JAMB Farfesa Ishaq Oloyede ya jajirce wajen dakile hanyoyin cin hanci da rashawa da satar amsa da gyara tsarin ilimi, abin da ya sanya Farfesa Hussaini Tukur, kwararre a fannin ilimi ya bayyana bukatar yi masa afuwa.
Makarkashiya ko kuskuren ma'aikatan JAMB?
Ko me hukumar JAMB ke tunanin yi da sauran dalibai da abin ya shafa da ke son a sake daukacin jarabawar, sanin cewa dalibai milyan 1.5 daga cikin 1.9 ne suka gaza samun maki 200 a jarabawar ? Farfaesa Ishaq Oloyede, shugaban hukumar ta JAMB ya ce: ‘'Daya ne daga cikin wadanda suka yi mana aiki bai sanya jarabawar a na'ura yadda ya dace ba, ba wai matsala ce ta na'ura ko makarkashiya ba''
Karin bayani: Hukumar WAEC ta samar da sabon tsarin rubuta jarrabawa
A kowace shekara, dubban daliban Najeriya ne ke fafutuka don cin jarabawar JAMB domin samun shiga jami'o'i, amma kalilan ne ke kaiwa ga nasara saboda matsaloli . Amma kwararru sun bayyana cewar akwai bukatar garambawul ga daukacin tsarin karatun bokon Najeriya don ya dace da ci-gaban zamani.