Jamus na zaton cewar guba ce aka bai wa Alexei Navalny
August 24, 2020Talla
Kakakin gwamnatin Steffen Seibert ya ce akwai alamun cewar Navalny guba ce aka ba shi ko da yake ya ce kawo yanzu ba su tantance ba. An kwantar da Alexei Navalny a ranar Alhamis da ta gabata a wani asibitin da ke a gabashin Rasha a Omsk kafin daga bisanin a mayar da shi a Jamus a karshen mako a bisa bukatar hukumomin Berlin. Tun farko sai da aka kwashe tsawon lokaci ana kai ruwa rana tsakanin iyalen sa da likitocin Rashar kafin su amince a tafi da shi zuwa Jamus.