Alakar Faransa da Isra'ila ta fara yin tsami
August 20, 2025Faransa da Isra'ila sun bude sabon babin tsamin danganta, bayan da Benjamin Netanyahu ya zargi shugaba Emmanuel Macron da kara rura wutar kyamar Yahudawa saboda aniyar da ya sanar ta amincewa da kafa kasar Falasdinu.
Karin bayani: Faransa za ta amince da Kasar Falasdinu
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya aike wa shugaba Emmanuel Macron wasika, inda ya nuna damuwa kan karuwar kyamar Yahudawa a biranen Faransa a 'yan shekarun nan tare da zargin hukumomin Paris da gaza daukar matakai na zahiri don dakile hakan.
Sai dai a fusace fadar shugaban kasar Faransa ta yi martani da kakkausar lafazi inda ta ce ko kadan babu kanshin gaskiya a wannan magana, sannan kuma shugaba Macron zai rubuta wa Netanyahu amsa nan ba da jimawa ba.
Karin bayani: Canada za ta goyi bayan kafa kasar Falasdinu
A karshen watan Yulin da ya gabata ne dai shugaba Macron na Faransa ya sanar da aniyar amincewa da kafa kasar Falasdinu, matakin da ya samu marawar wasu kasashen Duniya fiye da 10 ciki har da Canada da Australia.