A birnin Yamai na jamhuriyar Nijar an shirya wata gasa ta wake-wake ga matasa maza da mata inda a ciki ake son gano matashi ko matashiyar da ke da kwazo da kuma murya gami da basira ta rera waka a wani mataki na karfafa harkokin al’adun kasar ta Nijar a tsakanin matasa. Sanin kowa ne dai wakokin gargajiya, wakoki ne da ke kumshe da kalamai masu kayatarwa ko ma ma a ce da ke koyar da wasu darussa ga mai sauraronsu ta sabili da basirar da mawakan ke da ita wajen shirya wakokinsu.
Sai dai a wannan lokaci da ake ciki an ga cewa matasa sun baude sosai wajen aron al’adu, inda akasari suka yi watsi da nasu al’adun. Amma a wani mataki na waiwaye adon tafiya da kuma neman karfafa al’adun ta hanyar samar da matasa masu kwazo a fannin waka, ta sanya wani gidan talbijin mai zaman kanshi da ake kira Nijar 24, ya shiyar wata gasa wadda a cikinta matashi ko matashiyar da ta yi nasara zai iya samun tukuci har na jaka dari biyar tare kuma da bayar da tallafi na bi sau da kafa domin ganin ya samu cimma burinsa a fannin wake-wake. To wannan tsari da aka kirkiro don ganin matasa da ke da son shiga harkoki na wakoki sun samu kirkiro wakokinsu na kansu tare da karfafa al’adu na gida Nijar.