Alƙalan Nijar sun shiga yajin aiki
July 31, 2012Wannan dai shi ne karo na biyu cikin makonni uku da ƙungiyar alƙalan Nijar ke shiga yajin aikin, a ci gaba da takun sakar da ta soma da gwamnatin a game da jerin wasu kokekoke da ta ce ta shigar kusan shekara daya ke nan. sai dai kuma gwamnatin ta biya bukatun alƙalan ba, duk da alƙawarin da ta ɗauka a zaman tattaunawar da ya hada ɓangarororin biyu, kamar yadda mai shari'a Abdullahi Gube mataimakin magatakardar ƙungiyar alkalai ta jamhuriyar Nijar ya tabbatar.
Tun farkon hawan mulkin sabbin hukumomin jamhuriya ta bakwai,aka soma wani fiskantar zaman doya da man ja tsakanin kungiyar alkalan kasar ta Niger ta Saman da fadar muli ta Yamai. Hasali ma dai wasu kusoshin gwomnatin sun fito fili sun zargi wasu alkalan da kasancewa bata gari da ke gurbata fannin shari'a a Niger inda suke karbar cin hanci musamman tun bayan da shari'a ta sha wanke 'yan tazarce ko kuma basu beli.Tun daga wancan lokaci ne dai wasu ke kallon alkalan da kasancewa 'yan koran wasu yan siyasa.To amma da ya ke mayar da martani kan wannan batu babban sakataren ƙungiyar alƙalan ta SAMAN ya yi watsi da zargin inda ya ce ba shi da wani tushe da kuma makama.
Wannan yajin aiki ya yi matukar tasiri wajen dagula harkokin shari'a a Jamhuriyar Nijar inda kotunan da wakilin Deutsche welle ya ziyarta suka kasance a rufe. Jama'a da su ka je neman biyan bukata a kotunan ba tare da samun biyan bukata sun bayyana rashin jin daɗinsu game da halin da ake ciki. Sai dai har ya zuwa ranar talata da rana ma'aikatar sharIa ta Jamhuriyar Nijar da DW ta tuntuba domin jin ta bakinsu kan wanann yajin aiki na alkallai ba ta ce uffan ba. Amma kuma ta tabbatar da cewa su na shirin komawa kan teburin tattaunawa da alkalan nan ba da jimawa ba domin gano bakin zaren warware matsalar.
Mawallafi: Gazali Abdu Tasawa
Edita. Mouhamadou Awal