Akalla mutum 30 sun mutu a hatsarin kwale-kwale a DRC
June 12, 2025Akalla fasinjoji 30 ne ciki har da dalibai da dama suka mutu lokacin da jirgin ruwa ya nutse da su a arewa maso yammacin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango sakamakon rashin kyan yanayi .
Mazauna yankin da kuma kafofin yada labarai na kasar sun tabbatar da aukuwar hadarin a ranar Alhamis. Ana ci gaba da neman mutane da dama kuma har yanzu babu labarinsu tukunna.
Jirgin ruwa ya kama da wuta a tsakiyar kogi a Najeriya
Jirgin ruwan mai dauke da mutane da kuma kaya ya nutse ne a bakin Kogin Tumba a yankin Bikoro a ranar Laraba da dare.
Wani tsohon babban jami'in gwamnati da ya yi ritaya wanda ke zaune a garin Bikoro, José Ipalaka ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na The Associated Press cewa danginsa uku suna cikin wadanda aka tabbatar sun mutu.
Sojojin Afirka ta Kudu sun fara ficewa daga DRC
Hukumomi sun ce suna ci gaba da aikin ceto domin gano sauran mutanen da ba a san inda suke ba kuma za a sanar da iyalansu duk hali da suke ciki da zarar labari ya samu.