Akalla mutum 16 sun rasu a hadarin jirgin sama a Bangladesh
July 21, 2025Akalla mutane 16, mafi yawancinsu dalibai, sun rasa rayukansu a ranar Litinin bayan wani jirgin rundunar sojin sama ta Bangladesh ya fadi a cikin harabar wata makaranta a Dhaka babban birnin kasar.
Wannan lamarin shi ne mafi muni cikin hadurran jiragen sama da suka faru a kasar cikin shekaru da dama.
An gabatar da rahoton binciken farko na hadarin jirgin Air India
Wani mai daukar hoto na kamfanin dillancin labarai na AFP da ke wurin ya ce ya ga jami'an kashe gobara suna kwasar daliban da suka jikkata yayin da sojoji ke taimakawa wajen zakulo mutane daga cikin baraguzan jirgin da ya fadi.
Fiye da mutane 100 ne suka jikkata a hadarin, inda akalla 83 ke karbar magani a asibitoci daban-daban, in ji hukumomin kasar.
Bangladesh ta bukaci Indiya da ta mika mata Sheik Hasina
Jirgin na F-7 BJI da aka kera a kasar Sin ya tashi ne da karfe 1:06 na rana (07:06 GMT) kuma ya fadi jim kadan a harabar makarantar mai suna Milestone School and College.