Ta'azzarar fataucin kwayoyi tsakanin bakin haure a Agadez
April 30, 2025A Jamhuriyar Nijar, mutanen jihar Agadez sun nuna damuwa kan yadda bakin-haure da ke kan hanyasu ta zuwa ci-rani kan haifar musu da yawaitar sha da fataucin miyagun kwayoyi.
Agadez ta kasance magama ta shige da ficen 'yan ci-rani na kasashen Afirka ta Yamma, duk da cewar sun sake hanyoyi da suka saba bi ta kasachen Aljeria da Libiya da zummar wucewa Turai.
Harkar shige da ficen bakin hauren ya haifar da abubuwa marasa kyau a tsakanion wadanda walau ke kan hanyar tafiya ko kuma dawowa gida kuma ke yada zango a jihar ta Agadez. Matsalolin sun hada da safarar miyagun kwayoyi da na mutane da muma makamai da sauran su. Dr Sanda Malam Sofon mataimakin magajin garin Dirkou da ke a kan iyaka da kasar Libiya ya yi bayanin girman al amarin.
Wani batu da ke daukar hankali sosai shi ne, yadda ake tursasa wa mata 'yan ci ranin shiga aikin karuwanci a can kasashen Libiya da Aljeriya. Inda su kan su 'yan mata da matan da suka tsinci kansu cikin wannan yanayi kan yi nadamar ummul aba'isin barin kasashensu na asali da zummar neman tudun mun tsira a ketare.
Yawaitan shan kwaya da safararta dai shi ne abun da a yanzu yake ci gaba da ci wa al'ummar Agadez din tuwo a kwarya, musammam bisa la'akari da cewar, nan ne mahadar Afrika ta Yamma da kasashen Libiya da Aljeriya da ke kuma zama mashigin nahiyar Turai.