Afirka tana taka rawa kan makamashin da ake sabuntawa
August 21, 2025Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya ce kasashen Afirka suna da gagarumar rawar takawa wajen samar da makamashin da ake sake sabuntawa. Ya bayyana haka a wajen taron da ke gudana na kwanaki uku na shugabannin Afirka da ke wakana a kasar Japan.
Karin Bayani: Taron tattalin arziki tsakanin Japan da Afirka
Ita dai kasar Japan ta nuna kanta a matsayin wadda za ta iya sauya kasar China cikin nahiyar Afirka da ake fuskantar matsalolin bashi da kasashen nahiyar suka karba, ga kuma zabtare galibin taimakon kasashen Yammacin Duniya, kana matsalar sauyin yanayi take ci gaba da nuna kanta.
Akwai jiga-jigan shugabannin Afirka da suke halartar taron da suka hada da Shugaba Bola Tinubu, da Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kud gami da Shugaba William Ruto na Kenya.