Afirka ta Kudu za ta sake nazari kan ayyukan dakarunta a DRC
March 7, 2025Ministar tsaron Afirka ta Kudu Angie Motshekga ta shaidawa kamfanin dillancin labarai ne Reuters cewa kasarta ba ta yanke hukunci kan janyewar dakarun ko kuma akasin hakan ba, kasancewar su ke jagorantar sauran rundunonin yakin kasashen ketare da ke jibge a Kwango.
Karin bayani: Kabila ya caccaki Tshisekedi kan yakin Kongo
Ministar ta ce shugabanni da gwamnatocin kasashen Kudancin Afirka (SADC) da kuma na kasashen Gabashin Afirka za su hadu nan ba da jimawa ba domin tattaunawa kan makomar dakarun wanzar da zaman lafiyar kasashen Afirka da ke rangadi a Kwango.
Karin bayani: M23 ta kwace iko da babban filin jirgin saman Goma
Masu sharhi kan tsaro na ci gaba da sukar rawar da Afirka ta Kudu ke takawa a DRC, wanda har ya kai ga faduwar birnin Goma ga 'yan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Ruwanda.
.