Afirka: Shugabannin mutu ka raba
Shugabannin wasu kasashen Afirka sun kwashe tsawon shekaru a kan mulki, inda da yawa daga cikin 'yan kasarsu ba su san wani shugaba ba bayan su. Shugabannin da suka fi tsufa da dadewa, na kasashe makwabtan juna ne.
Equatorial Guinea: Teodoro Obiang Nguema
Teodoro Obiang Nguema da shekaru 46 a karagar mulki, ya kasance shugaban kasa a Afirka da ya fi kowa dadewa a mulki. Su biyu ne suka rike wannan mukamin mafi dadewa a kan mulki, har shekara ta 2017. Tare da Shugaba José Eduardo dos Santos na Angola, suka dare mulki a shekara ta 1979. A shekarar 2022, an sake zabar sa. A yanzu dansa da ya kasance mataimakin shugaban kasa, na jiran gadon kujerarsa.
Kamerun: Paul Biya
Shugaban Kamaru, shugaban kasar da yafi yawan shekaru a Afirka: An haife shi a 1933, Paul Biya na rike da mukamin shugaban kasa tun a 1982. Ya taba rike mukamin firaminista, na tsawon shekaru bakwai. A shekara ta 2008, an yi wa kundin tsarin mulkin Kamaru kwaskwarima da nufin bai wa Biya damar yin tazarce. A watan Oktobar shekara ta 2025, mai shekaru 92 a duniyar zai sake tsayawa takara.
Jamhuriyar Kwango: Shugaba Denis Sassou Nguesso
Tuni Shugaba Denis Sassou Nguesso ya kwaskware kundin tsarin mulki, domin samun damar yin tazarce. Ya hau kan mulkin Jamhuriyar Kwango (Congo Brazzaville) tun a 1979, an saka sake zabarsa a matsayin shugaban kasa a 2021, jam'iyyun adawa sun kauracewa zaben, kana kungiyar bishop-bishop ta kasar wato 'Bishops Conference', ta yi korafi kan sahihancinsa.
Yuganda: Shugaba Yoweri Museveni
Kusan shekaru 40 Yoweri Museveni ke kan madafun iko, 'yan kasarsa da dama ba su san wani shugaban kasa ba sai shi. Kaso 80 cikin 100 na al'ummar Yuganda miliyan 46, an haife su bayan ya dare kujerar mulki a shekarar ta 1986. Domin samun damar sake yin tazarce a 2012, mai shekaru 76 a lokacin Museveni ya rusa ka'idar shekarun shugaban kasa. Yana shirin sake tsayawa takara, a zaben 2026.
Eswatini: Sarki Mswati na III
Sarki Mswati na III ya jira shekarunsa su kai, kafin ya zama sarki. Mahaifinsa Sarki Sobhuza na II da ya yi shakru 61 yana mulki, ya rasu a 1982 a lokacin Mswati na III na da shekaru 14. Shekaru hudu bayan nan, Mswati na III ya dare mulki a matsayin cikakken sarki daya tilo a Afirka. Da fari ya yi mulki tare da mahaifiyarsa a 'yar karamar kasar ta Eswatini a matsayin Nndlovukazi "Babbar Giwa".
Iritiriya: Shugaba Isaias Afewerki
Karamar kasar da ke gabar Tekun Bahar Maliya, ba ta taba yin wani shugaban kasa ba. An nada Isaias Afewerki shugaban kasa a watan Mayun 1993, jim kadan bayan da 'yan Iritiriya suka zabi samun 'yancin cin-gashin kai a kuri'ar raba gardama. A baya ana yi wa mutumin da aka haifa a 1946, kallon mai kawo sauyi. A yanzu, duniya na masa kallon mai mulkin danniya da ya mayar da kasarsa saniyar ware.
Djibouti: Omar Guelleh
Shi ne na karshe da ya dare bisa mulki, kafin shekarun 2000. Shugaba Omar Guelleh na mulkin Djibouti, tun 1999. A tsawon wannan lokaci, ya yi amfani da yankin da yake na Daular Larabawa wajen bunkasa 'yar karamar kasarsa. A yanzu, Djibouti na zaman mai masaukin baki ga sansanin sojojin Amurka da Faransa da Japan da kuma Chaina.
Ruwanda: Paul Kagame
Tun 19 ga watan Yulin 1994, Paul Kagame ke mulki a Ruwanda. Ya fara rike mukaman mataimakin shugaban kasa da ministan tsaro. Bayan Shugaba Pasteur Bizimungu ya yi murabus, majalisar dokoki ta zabi Kagame ranar 17 ga watan Afrilun 2000 a matsayin magajinsa. Yayin wani zaben raba-gardama a 2015, ya yi nasarar soke wa'adin shekaru biyu na shugaban kasa. Kagame zai iya mulki, har zuwa shekara ta 2034.
Togo: Faure Gnassingbé
A 2005 Faure Gnassingbé ya karbi mulkin Togo daga mahaifinsa da ya kwashe shekaru 38 yana shugabancin kasar. Bayan gagarumar zanga-zanga da 'yan kasar suka yi, an samar da dokar da ta takaita wa'adin mulkin shugaban kasa a 2017. Tun a shekara ta 2025, Gnassingbé ne shugaban majalisar ministocin kasar. 'Yan adawa na sukar matakin da cewa, zai iya zama shugaban kasar mutu ka raba.