Labaran Afirka masu daukar hankali a jaridun Jamus
June 13, 2025Za mu fara ne da sharhin da Zeit Online ta yi kan kalubalen tsaron a kasashen Afirka, mai taken "Sojojin haya na Wagner za a maye gurbinsu da Afrika Korps na Rasha", inda ta ce Wagner ta janye daga Mali a hukumance, amma dakarunta na haya da dama za su ci gaba da zama a kasar. A tsokacin da ta yi, jaridar ta ce gwamnatin mulkin sojin Mali na ci gaba da dogaro a kan Rasha a matsayin abokiyar kawance a ayyukan yaki da ta'addanci a yammacin Afirka.
Zeit Online ta ce tun bayan juyin mulkin 2000 da 2001, gwamnatin mulkin sojan Mali ta katse hulda da Faransa da ta yi wa mulkin mallaka tare da samun goyon bayan Wagner a fannin tsaro. Ita kungiyar ko rundunar ta ba da gudunmawa a yaki da ta'addanci tare da tabbatar da tsaron masu rike da madafun iko, da bayar da horon soja. Amma dai, a cewar jaridar, har yanzu Mali ba ta tabbatar da kasancewar sojojin haya na Wagner a hukumance ba, amma za ta ci gaba da aikin hadin gwiwa da sojojin Rasha.
Yanzu kuma sai batun cin zarafi da tauyen 'yancin fadan albarkacin baki a Kenya, inda die tageszeitung ta ce "Sukar gwamnatin Kenya a kafofin intanet na jefa rayuwar 'yan kasar cikin hatsari" na kamawa ko na kisa. Jaridar ta ce wani mai fafutuka ta yanar gizo ya mutu a hannun 'yan sanda a Kenya. Albert Omondi Ojwang, malamin makaranta mai shekaru 31 da haihuwa, an kama shi ne a garin Homa Bay da ke yammacin kasar Kenya bisa zarginsa da sukar mataimakin kwamishinan 'yan sanda Eliud Lagat ta yanar gizo.
Die tageszeitung ta kara da cewa, Albert Ojwang ba shi ne dan gwagwarmaya ta kafofin sada zamunta na farko da aka kama a baya bayan nan a Kenya ba. Ko a zanga-zangar da aka yi wa lakabi da "Generation Z" ta adawa da karin haraji mai cike da cece-kuce, 'yan sanda sun kashe sama da mutane 50, da yawa daga cikin su masu fafutuka ta yanar gizo, ko kuma suka yi bata dabo, bisa laifin yin amfani da bayanan karya a yanar gizo da kuma cin mutuncin jami'an gwamnati a shafukan sada zumunta.
Ana nata bangaren, Frankfurter Allgemeine Sonntagszeitung ta mayar da hankali kan taimakon da gwamnatocin Afirka suke samu daga ketare don samar da layin dogo a kasashensu. A cikin sharhinta mai taken "Africa Express", jaridar ta ce ko da yake samun kudi daga kasar Sin ba abu ne mai sauki ba, amma wannan kasa na ci gaba da zuba jari a hanyoyin jiragen kasa na nahiyar Afirka, domin samun dama cin gajiyar albarkatun karkashin kasa tare da tsere wa kasashen Yamma.
Jaridar da ake wallafawa a birnin Frankfurt ta ce layukan dogo a Afirka sun kasance hanyoyin sufuri da Turawan mulkin mallaka suka yi amfani da su. Amma a yanzu, hanyoyin jiragen kasa sun kasance kashin bayan zuba jari na kasar Sin a Afirka, saboda suna hade wurare masu mahimmanci, amma suna da tsadar samarwa. Frankfurter Allgemeine Sonntagszeitung ta kara da cewa kudi ya yi karancin a birnin Beijing, kuma kasashen Afirka kamar Zambiya sun fada cikin matsalar bashi, amma saboda muhimman albarkatun kasa, Sin ta ci gaba da yin hobbasa a fannin layin dogo.
Za mu karkare da die tageszeitung da ta karkata ne kan manufofin shige da fice tsakanin Amurka da kasashen Afurka, inda ta ce matakin haramcin shiga Amurka na Donald Trump da ya shafi kasashen Afirka da dama ya fara aiki, duk da kakkausar suka da ya janyo musamman ma a Afirka. Jaridar da ake wallafawa a kullum ta ce 'yan Equatorial Guinea, Iritriya, Kongo-Brazzaville, Libiya, Somaliya, Sudan, da Chadi ba su da izinin shiga Amurka kwata-kwata, saboda matafiya daga kasashen da abin ya shafa na haddasa barazanar tsaro, a cewar fadar mulki ta White House.
Sai dai, die tageszeitung ta yi misali da kasar Saliyo da makwabciyarta Laberiya da ke da dangantaka ta kut-da-kut da Amurka, amma suke haifar da damuwa a fannin tsaro, saboda matafiyansu na wuce lokacin da bizarsu ta kayyade musu a Amurka. Jaridar ta ce dalibai daga kasashen da abin ya shafa na fuskantar barazanar soke bizarsu. Amma yawancin 'yan Afirka ba su da niyyar ba da kai bori ya hau, inda gwamnatin Chadi ta ba da sanarwar hana bisa ga 'yan Amurka.