Afirka a Jaridun Jamus 15.08.2025
August 15, 2025Jaridar die tageszeitung ta ce, makwanni kadan da suka gabata ne aka rattaba hannu kan wasu yarjejeniyoyin kawo karshen yakin da ake yi a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango. Amma yanzu fada ya sake barkewa ta kowane bangare. A cikin 'yan kwanakin nan, sojojin kasar sun yi artabu da 'yan tawayen M23 a lardin Kivu ta Kudu da ke gabashin Kwangon.
Wasu gungun mayakan sakai na Wazalendo na yankin da ke fafatawa tare da sojoji, sun sun doshi babban birnin lardin Bukavu, wanda kungiyar M23 ke iko da shi tun a watan Fabrairu, kuma an yi ta luguden wuta. Kazalika an yi taho-mu-gama a lardin Kivu da ke makwabtaka, inda 'yan kungiyar ta M23 ke da sansanoninsu na tarihi tare da kwace babban birnin lardin Goma a watan Janairu.
'Yan tawaye da sojoji na zargin juna da kin bin yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma. A cikin watan Yuli ne bangarorin biyu da ke rikici da juna suka rattaba hannu kan wata yarjejeniya a Doha babban birnin kasar Katar, wadda ke da nufin aza harsashin cimma cikakkiyar yarjejeniyar zaman lafiya. Yarjejeniyar ta hada da tsagaita wuta da musayar fursunoni.
"Cote d'Ivoire ta sake zama matattarar rikici" wannan shi ne taken sharhin da jaridar Süddeutsche Zeitung ta wallafa. Inda ta ce a watan Oktoba, Shugaba Alassane Ouattara na son a sake zabensa a karo na hudu. Ba a yarda manyan abokan hamayyarsa su tsaya takara ba, kuma yanzu magoya bayansu suna kan tituna.
Bisa dukkan alamu zaman lafiya da aka samu tun bayan kawon karshen yakin basasa a shekara ta 2011 ya zo karshe. A dai-dai lokacin da za a gudanar da zabuka a watan Oktoba, sabbin tashe-tashen hankula na siyasa sun kunno kai, wadanda ke tunatar da yakin basasar da aka yi a baya. A watan Yuli ne dai Shugaba Alassane Ouattara mai shekaru 85, kuma ke kan karagar mulki tun shekara ta 2011, ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takara a zaben ranar 25 ga watan Oktoba, sanarwar da ta tayar da hankali a Cote d'Ivoire.
Hakan ba zai kasa nasaba da cire duk masu adawa da muhimman 'yan siyasa daga zaben ba. Dan takarar da ya fi daukar hankalin jamaa shi ne tsohon maaikacin banki Tidjane Thiam, wanda ya so ya tsaya takara a babbar jamiyyar adawa ta PDCI, amma shaidar kasancewarsa tsohon dan kasa na Faransa ya hana shi daman takara.
Sai kuma muhimmin dan siyasa kuma tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo, wanda Ouattara ya gaji kujerarsa kuma ya ki amincewa da shan kaye a kan Ouattara a shekara ta 2010, lamarin da ya janyo yakin basasa na tsawon watanni hudu da ya yi sanadin mutuwar dubban mutane, amma kotun hukunta manyan laifuka da ke Hague, ta wanke shi daga bisani, inda ya dawo kasarsa kuma ya kafa sabuwar jam'iyya, PPA-CI (Jam'iyyar Mutanen Afirka ta Ivory Coast).
Za mu karkare ne da jaridar Zeit Online wadda a sahrhinta ta ce "Me ya sa kowa ke maganar yunwa a Gaza amma ba a maganar Sudan? Tambaya ce mai ma'ana. A halin yanzu, babu abun da ya fi daukar hankalin kamar zanga zangar goyon bayan Falasdinawa.
A cewar jaridar rashin nuna daidaito a tsakanin al'ummar duniya yana da ban mamaki. Amma da farko, zanga-zangar adawa da laifukan da Isra'ila ke yi a Gaza ya dace kuma ya zama dole. Na biyu, yana kuma da muhimmanci a kula da bukatun al'ummar Sudan. Ayar tambaya ita ce, me yasa hankali ya karkata daga Sudan? Saboda wannan yakin ya zama mai rudani? Domin 'yan gudun hijirar Sudan kadan ne ke zuwa Turai? Ko kuma saboda kasar tana cikin nahiyar Afirka, inda a kullum suke cikin yake yake da rikici da bala'i? Duk wadannan nan haka suke a zahiri, amma ba su isa zama hujja na watsi da yakin Sudan ba.