Afghanistan: Ambaliyar ruwa ta yi sanadin rayuka da dama
May 19, 2024Talla
Jami'an 'yan sanda sun ce kawo yanzu ana ci gaba da neman wasu da dama da ruwan ya yi awon gaba da su kana babu wasu alkalumma na wadanda suka jikkata a iftila'in.
A cewar shugaban sashin yada labarai na lardin Ghor, Mawlawi Abdul Hai Zaeem daruruwan hectar filayen noma ne suka lalace, yayin da ambaliyar ta kuma lalata gidaje fiye da 2,000 a babban birnin lardin, Feroz-Koh.
Karin bayani: Afghansitan: Ambaliya ta halaka mutane
Iftila'in dai na zuwa ne a daidai lokacin da Afghanistan din ke kokarin farfadowa daga ambaliyar ruwan da ta auku a arewacin Lardin Baghlan a makon da ya gabata, inda jami'ai suka tabbatar da mutuwar mutane a kalla 315 yayin da wasu 1,600 suka jikkata.