Ko kasashen AES za su tsaya da kafafunsu?
June 4, 2025Makasudin taron dai shi ne taimakon junansu a fannin kiwon lafiyar da ke cike da tarin kalubale, musamman a yankunan da ke fama da matsalar tsaro. Taron kiwon lafiyar kasashen na AES ya tattauna batun samar da matakan bai daya, na tunkarar matsalolin kiwon lafiya da ke addabar al'ummomin kasashen AES din wato Jamhuriyar Nijar da Mali da kuma Burkina Faso da nufin samo mafitar magance su.
Matakin na karkashin sabuwar tafiyar hadin gwiwa da neman cikakken 'yancin kai a kowane fanni na rayuwa bayan ficewarsu daga kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma wato ECOWAS ko CEDEAO. A jawabinsa na bude taron, firaministan Jamhuriyar Nijar Mahaman Ali Lamine Zeine ya ce wannan shirin da kasashen AES din suka bijiro da shi na da muhimmancin gaske. Kasashen sun bijiro da wannan shiri na neman hada kai a fannin kiwon lafiya ne, domin maye gurbin tsarin da suke kai a lokacin suna cikin kungiyar ECOWAS ko CEDEAO a cewar Dakta Halarou Chefou daya daga cikin kwararrun jami'an kiwon lafiya da ke halartar taron daga Nijar.
Wannan mataki na karfafa hulda a fannin kiwon lafiya tsakanin kasashen na AES na zuwa ne, a daidai lokacin da kasashen ke fuskantar matsalar tsaro a tsakanin iyakokinsu. Amma a cewar kwararren jami'in kiwon lafiya daga kasar Mali Dokta Bouyagui Traore wannan shirin na yanzu, zai samar wa da matsalar tsaron magani. A karshen zaman taron dai mahalartan nasa sun fitar da jerin shawarwari na yadda za kasashen na AES za su karfafa huldarsu a fannin kiwon lafiyar, shawarwarin da za su gabatar da su a gaban taron shugabannin kasashen kungiyar na gaba.