Adadin wadanda suka mutu a Afghanistan sun karu
September 5, 2025Talla
Adadin wadanda suka mutu sakamakon girgizar kasa mai karfi da ta afku a ranar Lahadi a gabashin Afghanistan ya haura mutum 2,200, a cewar hukumomin Taliban.
Rahotannin sun ce sama da mutane 4,000 sun jikkata, galibinsu a lardin Kunar da ke iyaka da Pakistan.
Lamarin ya shafi sama da mutane miliyan 1.3, tare da lalata ko ma rushe daruruwan gidaje.
Girgizar kasar mai karfi 6.0 a ma'aunin richter ta kasance mafi muni cikin shekaru masu yawa.
Ayyukan ceto sun samu cikas sakamakon fadowar duwatsu da kuma kasa, yayin da kungiyoyin agaji ke gargadin cewa bukatar taimakon jinkai na karuwa cikin gaggawa.