SiyasaTurai
Adadin attajiran Landan na raguwa sakamakon haraji
April 9, 2025Talla
Wani rahoto daa Cibiyar Tattara Alkaluman Attajirai na Duniya ta fitar ya bayyana cewa dubban attajiran birnin Landan na kasar Burtaniya sun fice daga kasar zuwa Amurka da Asiya domin kauracewa biyan tarin haraji ko kuma tasirin ficewar Burtaniya daga EU.
Karin bayani: An tono asirin manyan attajirai da shugabanni
Jaridar Times ta rawaito cewa masu bai wa attajiran shawara kan haraji, na basu tabbacin samun sauki na biyan haraji a kasashen Portugal da Spain da Girka Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Italiya. Kazalika rahoton ya ce adadin attajiran na birnin Landan ya ragu matuka daga 227,000 a 2023 zuwa 215,700.