Salon rayuwa
Abu Namu: Zama gida guda tsakanin ma'aurata da surukai
Lateefa Mustapha Ja'afar MNA
February 3, 2020Talla
Nazari kan wani sabon salon bautar da yara da ake aurarwa da kananan shekaru a kuma kai su zama da surukai ko kishiyoyi, abin kuma da ake alakantawa da yawan mace-macen aure da ma guje-gujen matan da surukai ko kishiyoyi ke azbtarwa ta hanyar sanya su ayyukan da suka fi karfinsu a cikin gida, wadanda da zarar sun kwanta ma ba su da lokacin mazajensu ko kula da 'ya'yansu. Mata da dama ne dai ke tsintar kansu cikin irin wannan matsalar.