Abu Dhabi ta gargadi Isra'ila kan yankunan Falasdinawa
September 3, 2025Mahukuntan na Abu Dhabi sun bayyana matakin da na wuce gona da iri da ma rushe yarjejeniyar da aka cimma ta Abraham Accord ta kyautata dangantaka a tsakanin kasashen biyu da wasu na Larabawa, karkashin jagorancin shugaban Amurka Donald Trump.
Wannan dai shi ne karon farko da kasar ta Hadaddiyar Daular Laraba ke fitowa karara tana sukar Isra'ila a kan matakinta a yankunan Falasdinawa tun bayan barkewar yaki a tsakanin su da mayakan Hamas.
Mataimakiyar ministar harkokin kasashen ketare ta Abu Dhabi Lana Nusseibah ta sake jaddada matsayarsu ta tun shekarar 2020 a kan kin amincewa da mamaye yankunan Gabar Yamma da Kogin Jordan kuma ta ce ba za su sauya ba.
Isra'ila dai duk da sukar da take sha daga kasashen duniya ciki harda wadanda suka goya mata baya na kasashen EU, tana ci gaba da luguden wuta tare da tarwatsa al'ummar Gaza.
Karin Bayani:Isra'ila za ta fadada matsugunan Yahudawa