Libiya: Firaminista zai tsaya takara
November 21, 2021Talla
Wannan dai na zuwa ne bayan da a baya Abdulhamid al-Dbeibah mai shekaru 63 a duniya ya sha alwashin ba zai yi takara ba, matakin da ya ba shi damar darewa kujerar firaministan da yake kai a yanzu. Ana ganin wannan matakin shiga takarar da firaministan ya yi, ka iya janyo wani sabon rikici.
Da ma dai Firaminista al-Dbeibah na daga cikin masu adawa da dokar da kakakin majalisar dokokin Libiyan Aguila Saleh ya samar, na yin zaben a karshen wannan shekarar. Wannan zabe na Libiya na da matukar muhimmanci, inda ake fatan zai kawo karshen rikicin da kasar ta kwashe tsawon shekaru 10 tana ciki.