Abdallah II ya yi tir da mamaye Gabar Yamma da Kogin Jordan
September 7, 2025Sarki Abdallah II ya sanar da hakan a yayin wata ziyara da ya kai Hadaddiyar Daular Larabawa, biyo bayan matsayar da gwamnatin Isra'ila ke kokarin dauka na fadada matsugunan Yahudawa a Gabar Yamma da Kogin Jordan, gabanin taron zauren Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York na Amurka, wanda kasashe da dama suka tabbatar da goyon bayan kafuwar kasar Falasdinu.
Karin bayani:Isra'ila ta kai farmaki gabar yamma
Shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa Mohammed bin Zayed Al Nahyan ya bi sahun Sarki Abdallah II wajen yin fatali da bukatar Isra'ila, wanda ta fara tun daga 1967.
Karin bayani:EU ta bukaci dakatar da farmakin Isra'ila a yamma da kogin Jordan
Tun da fari dai Ministan Harkokin Wajen Isra'ila Gideon Saar ya gargadi kasashen Yammacin duniya kan kudurinsu na amincewa da kafuwar kasar Falasdinu, wanda hakan ka iya maida hannun agogo baya tare kuma da ingiza Isra'ilan kan daukar mataki a kan mazauna Gaza.