A yau ne ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe ga abinci
October 16, 2012
A daidai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ta ke tuni da zagayowar ranar da aka kebe ga abinci,milyoyin jama'a ne ke fama da yunwa da kuma karancin abincin a duniya. Tuni dai alkaluma suka bayana cewar sama da milyon 870 ne na jama'a ke fama da yunwa a duniya galibinsu kwa a kasashe 'yan rabana ka wadata mu irinsu nahiyar Afrika da kuma Aziya. To saidai hukumar da ke kula da cimaka ta duniya wato FAO, ta danganata wannan matsalar ne da dimamar yanayi a duniya abunda ke haddasa ambaliyar ruwa,kamarin hamada,da kuma karancin ruwa a wadansu lokuttan.
A yayin wannan ranar da aka kebe hukumar kulla da cimaka ta duniya wato FAO zata gudanar da wata mahawara a birnin Roma na Italiya a wannan Talatar wace zata hada sama da kasashe 45 na duniya domin duba yuyuwar rage parashin cimaka a duniya a daidai lokacin da jama'a ke cikin bukata.
Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita : Umaru Aliyu