El-Rufai ya ki karba kiran 'yan sanda
September 8, 2025Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufai, ya gaza halartar gayyatar da rundunar 'yan sanda ta jihar ta yi masa tare da wasu jiga-jigan jam'iyya guda shida.
Sai dai maimakon haka, ya aike da tawagar lauyoyinsa bakwai tare da shugaban jam'iyyar ADC na jihar, Elder Patrick Didan Manbut, domin wakiltar su a tattaunawa da jami'an tsaro kan tuhumar da ake yi musu.
Rahotanni sun ce rundunar ta kira tsohon gwamnan da sauran shugabannin jam'iyyar ne kan zargin cewa wasu kalaman da aka yi a taron jam'iyyar ADC a makon da ya gabata na iya tayar da tarzoma da barazana ga zaman lafiya.
A yayin zaman, Elder Patrick ya tabbatar da cewa sun je a madadin dukkanin wadanda aka gayyata, ciki har da tsohon gwamna El-Rufai, domin amsa tambayoyi kan tuhume-tuhumen da ake yi musu :
"Mun zo ne saboda umarnin da aka ba mu, kuma idan akwai sauran bayanai ko karin gayyata, za mu sake dawowa kamar yadda doka ta tanada.”
Wasu masu yin sharhi kan harkokin siyasa, ciki har da Mohammed Yaba, sun yi kira da a samar da hanyoyin tattaunawa don kawo karshen wannan takaddama. Sun ce tun da El-Rufai ya tura wakilai, hakan na nuna cewa ya mutunta gayyatar, kuma akwai buƙatar a yi amfani da wannan damar wajen samar da fahimtar juna.