Kiran al'ummar Nijar domin sako Moussa Tchangari
April 10, 2025Kwani tashi dai jagoran kungiyar nan mai fafutukar kare hakin jama'a da ci gaban karkara ta Alternative Espace Citoyen Moussa Tchangari, ya shafe sama da watanni hudu yana tsare a hannun hukuma.
Inda a halin yanzu yake a can gidan kaso na garin Filingue da ke a nisan kilomita kimanin 180 da birnin Yamai. don haka ne ta la'akari da kiraye-kirayen da 'yan kasa suka yi yayin babban zaman taro na kasa na a sallami duk wadanda ake tsare da su ta sabili da ra'ayoyinsu mabambamta.
Kungiyar ta Alternative ta yi amfani da wannan dama domin kira ga hukumomin na Nijar da su saki jagoran kungiyar Moussa Tchangari, da ke tsare ba tare da an yi masa shari'a ba wanda ta ce zargin da ake yi masa ya saba da akidar da yake da ita ta son ganin Nijar ta bunkasa a fannoni da dama.
A hannu daya kuma kungiyar ta Alternative Espace Citoyen ta fitar da wata takarda da ake kira pétition da za ta wallafa don duk wani mai son a saki Tchangari ya sa hannun ta yadda dubban Jama'a za su sa baki wajen neman a saki dan kungiyar faran hula.