An kaddamar da rajistar masu kada kuri'a a Somaliya
April 15, 2025Rahotanni daga birnin Mogadishu na cewa, Somaliya ta kaddamar da rajistar masu kada kuri'a na farko cikin shekaru 50, a wani mataki na dawo da kasar kan turbar dimokuradiyya gabanin babban zaben shugaban kasar da na 'yan majalisar dokoki da za a gudanar a 2026 a kasar da ta shafe shekaru a rikici.
Karin bayani: Masar ta kara bai wa kasar Somaliya manyan makaman yaki.
A bara ne dai shugaban kasar Hassan Sheikh Mohamud ya sanar da cewa lokaci da ya yi da ya kamata a kawo karshen dauki-dora da ake yi wajen zaben shugabanni a kasar tun daga 1969.
Karin bayani:WFP na jan hankali kan barazanar 'yunwa
Wakilin kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito cewa dubban mutane ne suka yi dafifi a rumfunan rajistar katin masu kada kuri'a da ke yankin Shangani na birnin Mogadishu. Ministan Yada Labaran Somaliya Daud Aweis ya wallafa a shafinsa na X cewa mutane da dama sun yi rajistar masu kada kuri'a kamar yadda kowanne 'dan adam ya kamata ya samu 'yancin gudanar da zabe.