Najeriya ta lashe kofin WAFCON karo na 10
July 27, 2025Tun da farkon wasan dai Moroko ce ke jagorancin wasan, inda kafin aje hutun rabin lokaci ta yi wa Najeriya ruwan kwallaye biyu a ragarta. Wannan lamari dai ya sanyaya gwiwar 'yan kallo da dama, har ma suke ganin ba lallai su kai ga samun nasara ba a wasan. Ko kafin a dawo hutun rabin lokaci, galibin 'yan kallon sun cika rigarsu da iska don gudun kada su tashi ba ga dare ga rashin nasara. Sai dai wasu kalilan sun yi ta maza, har kuma nasarar ta samu a kan idanunsu.
Karin Bayani: 'Yan matan Najeriya sun kai mataki na gaba
Wannan wasu ya zama tamkar daukar fansa kungiyar matan Najeriyar ta Super Falcons ta yi bayan rashin nasarar da ta samu a kan Morokon a shekarar 2022, inda Morokon ta yi waje da ita a wasan dab da na kusa da na karshe a gasar. Guda daga cikin 'yan kallon da suka tsaya aka kammala wasan a kan idonsu Usman Musa Murya ya bayyana cewa, wasan na da matukar muhimmanci.
Wannan nasara dai ta nuna cewa Super Falcons ta ci gaba da zama a matsayinta na jagora a fagen kwallon kafa a nahiyar Afirka, domin kuwa babu wata kasa da ta kai ta yawan lashe gasar cin kofin kasashen Afirkan. Shamsiyya Isa ta ce tun ba yanzu ba, babu wata tawaga ko ta maza ko ta mata da take zuwa kallonsu hankali kwance kamar ita Super Falcons. A cewarta tun da ta fara bibiyarsu har kawo yanzu ba su taba bata kunya ba, sai dai kawai idan rashin nasara ya zo wanda wannan kuma da ma haka al'dar wasa da ma rayuwa ta ke.
Karin Bayani: Kalubalen kwallon mata a yankin Hausawa
Kyaftin din Najeriya Rasheedat Ajibade ce ta lashe kyautar 'yar wasa mafi kwazo, yayin da mai tsaron ragar Najeriyar Chiamaka Nnadozie ta lashe ta mai tsaron raga mafi kwazo, ita kuwa Ghizlane Chebbak ta Moroko ta lashe kyautar 'yar wasan da ta fi zura kwallaye a raga. Bayan zama zakara a Afirka kuma yanzu hankalin tawagar ta Falcons za ta koma ne ga gasar cin kofin duniya, domin nan ma ta dasa dan ba kasancewar shi ne abinda ya gagare ta zuwa yanzu.