Kalubalan da ke a gaban sabon shugaban banki AfDB
September 2, 2025Sai dai kwana guda bayan rantsar da jagoran AfDB a hedkwatar cibiyar ta kudi da ke Abidjan na kasar Cote d'Ivoire, Ould Tah na jan aiki a gabansa wajen tallata manufofin bankin raya kasashen Afirka da kuma cimma burin da ya sa a gaba,
An kafa bankin raya kasashen Afirka ne a shekarar 1963 a birnin Khartoum na Sudan, inda da farko ya fara kunsar kasashe mambobi 23 na Afirka kafin daga bisani a 1965 a mayar da hedkwatarsa zuwa Abidjan da ke zama cibiyar cinikayyar Côte d' Ivoire.
Babban nauyin da aka dora wa bankin ADB shi ne rage talauci a kasashe mambobi ta hanyar ba da gudummawa ga ci gaban tattalin arzikinsu da ci gaban zamantakewa ta hanyar samar da ababen more rayuwa. Saboda haka ne bankin raya kasashen Afirka ya dogara kan cibiyoyin kudi uku don cimma manufofinsa, ciki har asusun raya Afirka, da asusun musamman na Najeriya.
A tsakanin shekarar 2015 zuwa 2025, bankin raya kasashen Afirka AfDB, karkashin shugabancin dan Najeriya Akinwumi Adesina, ya samu nasarar samar da kudade don gudanar da ayyukan raya kasa da dama a fannin noma, da makamashi, da kiwon lafiya, da samar da ruwa mai tsafta, da samar da sauran ababen more rayuwa. Hasali ma dai, fiye da mutane miliyan 550 ne suka ci gajiyar ayyukan bankin, ciki har da mata miliyan 231, kamar yadda shugaban AfDB mai barin gado ya bayyana a lokacin da yake waiwaye kan gudunmawar da ya bayar.
Sai dai har yanzu da doguwar tafiya a gaban AfDB, inda ayyuka da dama ke jiran sabon shugaban bankin raya kasashen Afirka kuma tsohon ministan tattalin arziki da kudi na Moritaniya Sidi Ould Tah. Amma, zai iya amfani da kwarewar da ya samu a kasarsa ta haihuwa a matsayin ministan kudi da kuma lokacin da ya rike matsayi mafi mahimmanci, a bankin Larabawa don ci gaban Afirka (Badea), inda ya yi nasarar kara yawan kudaden da ake kashewa har sau takwas.
Modibo Mao Makalou, masanin tattalin arziki dan kasar Mali kuma tsohon mai bai wa shugaban kasar Mali shawara kan harkokin tattalin arziki, ya ce akwai kalubale da Sidi Ould Tah zai iya fuskanta a bankin raya kasashen Afirka idan aka yi la'akari da burin da aka sa a gaba.
"Na farko shi ne, ya sake tsarin hada-hadar kudi a Afirka. Dole ne bankin raya kasashen Afirka ya bullo da dabaru na matsakaicin zango da za a cimmawa a cikin shekaru goma masu zuwa, wanda a zahiri suka dogara a kan ginshikai guda hudu. Na biyu shi ne, sarrafa yawan jama'a da nahiyar ke da shi zuwa abu mai amfani, musamman a fannin masana'antu da habaka albarkatun kasa a Afirka. Don haka, babban aiki ne, amma wanda ba zai gagari sabon shugaban AfDB ba."
Kudin da bankin raya kasashen Afirka ke tafiyarwa na fitowa ne daga gudummawar da kasashen Afirka 54 suke bayarwa, da mambobi a matsayin kungiyoyin raya tattalin arzikin yankin irin su ECOWAS da CEWAC, da kuma kasashe 28 da ba su da alaka da Afirka, da suka hada da Jamus, da Kanada, da China, da Amurka, da Faransa, da Japan, da kuma Birtaniya. Sai dai ana sa ran cewar AfDB zai rasa goyon bayan babbar mai ba da taimako, wato Amurka, bayan da fadar White House ta sanar da dakatar da tallafin da ta ke bayarwa, wanda aka kiyasta ya kai dala miliyan 555, a cikin kudirin kasafin kudinta na shekarar 2026.
A cikin shekaru 60 da kafuwa, jarin bankin raya kasashen Afirka ya karu inda ya tashi daga dalar Amurka miliyan 250 zuwa dalar Amurka biliyan 318, wanda hakan ya sa shi zama babbar cibiyar ciyar da kasashen Afirka gaba a fannin tattalin arziki.