Ƙasashen Turai sun shiga tsaka mai wuya
October 25, 2011Ƙasashen ƙungiyar Taraya Turai na cigab ada faɗi tashin lalubo hanyoyin warware matsalolin kuɗi da wasu ƙasashen membobi ke fuskanta.Ranar Lahadin da ta wuce shugabain sun shirya taro a birnin Brussels ba tare da cimma matsaya guda ba, sannan a wannan Larabar za su sake haɗuwa da zumar cimma yarjejeniyar bai ɗaya, game da hanyoyin magance matsalar kuɗin Girka da ta bankunan ƙasashen Turai.
Matsalolin bassusuka da wasu ƙasashenTurai ke fama da su,da durƙushewar bankuna ba ma kariyar darajar takardar kuɗin Euro na matukar tayar da hankalin shugabanin ƙasashen EU, wanda a cikin 'yan kwanaki nan suka matsa shirya taruruka da zumar fita daga wannan ƙangi.Bayan haɗuwar da suka yi ranar Lahadi, a wannan Larabar ma shugabanin suna shirya wata ganawa, dake matsayin zakaran gwajin dafin haɗin kai tsakanin ƙasashen Turai.
Manyan batutuwan da ke ajendar taron,sun haɗa da matsalolin bashin ƙasar Girka da kuma hanyoyin zuba zuzurunta kuɗaɗen ceton bankuna wanda suma su ka fara fuskantar matsaloli.
A tunanin Michael Hüther, shugaban cibiyar nazarin tattalin arzikin Jamus, ya zama cilas shugaban EU su cimma daidaito a taron na wannan Laraba:
"Akwai batutuwa da dama bisa teburinshawara, wanda ya zama wajibi a samu yarjejeniya kansu.Idan a ka samu wannan nasara, to suma kasuwanin hada -hadar kuɗi za su sarara."
Shima Michael Heise sugaban Allianz-Group ɗaya daga manyan kafofin kuɗi na duniya, bai yanke ƙaunar ganin an cimma nasara ba, domin a cewar sa matsalar idan aka zuba mata ido za ta kasance tamkar gobara daga kogi:
"A tunanina har ma an ɗan fara samun nasara hawa bisa turba kyakkyawa.Akwai shawarwari da dama, wanda za su taimaka a gano bakin zaren warware matsalar. Na yi imani ba ta zama gagarabadau ba."
Su dai ƙasashen Faransa da Jamus, dake matsayin shika-shikan ƙungiyar Tarayya Turai, har yanzu ba su cimma daidaito ba, game da asusun nan na Tarayya ,wanda EU ta ɗorawa yaunin ceton ƙasashen da talauci ya rutsa da su.Faransa ta buƙaci a ƙara yawan kuɗaɗen wannan asusu, wanda a yanzu suka tashi euro miliyan dubu 440, sannan a ɗaya wajen, hukumomin Paris sun shawarci ɗaiɗaikun kamfanoni, su sayi wani sashe na bassusukan da aka tambayo Girka, haka su kuma bankuna, sun rungumi ƙaddara su yafe wani sashe na wannan ɗimbin bashi, matakan da a cewar Jamus ba zata sabu ba wai bidiga a ruwa.
Masanin tattalin arziki Michael Heise, ya danganta wannan mataki da ruɓɓaɓar dubara:
"Wannan mataki zai kasancewa tamkar gyaran ijiyar biri, kawai zai ƙara cusa haɗari da zullumi cikin al´amura, saboda haka, sai an yi takatsantsan".
A halin da ake ciki dai, masana harkokin tattalin arzikin na ta hasashe game da sakamakon taron na shugabanin EU, wanda a cewar su, idan har bai haifar da ɗa mai ido ba, to zai jefa ƙasashen Turai cikin wani yanayi na tsaka mai wuya.
Banda ƙasar Girka da ta riga ta faɗa tsundum cikin matsala, shugabanin EU ,sun nuna damuwa game da halin da itama ƙasar Italiya ke shirin shiga.
Ta la´kari da wannan ɗauki ɗaiɗaya da talauci ke wa ƙasashen Turai, Firaministan Birtaniya David Cameron, ya shawarci Majalisar Dokokin ta kaɗa ƙuri´a fitar kasar daga rukunin ƙasashen EU,a matsayin matakin idan gemun ɗan uwanka ya kama da wuta ka shafawa naka ruwa.
Kuna iya sauraran rahotani biyu game da fafatukar EU na warware matsalar kudi, sai kuma na biyu wanda Sani Dauda ya aiko daga Landan game da yunƙurin Birtaniya na fita daga EU.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Umaru Aliyu