Ƙaruwar 'yan gudun Hijira zuwa nahiyar Turai
February 26, 2011Rahotanni daga Libya dai na nuni da cewar a yanzu haka yankin gabashin birnin Tripoli na karkashin ikon 'yan adawan adaidai lokacin da arangama ke cigaba tda gudana tsakanin magoya bayan shugaba Moammar Gaddafi da masu adawa. Al'ummomin ƙasashen waje da ma 'yan asalin Libyan dai na cigaba da ficewa daga ƙasar. Manazarta sun jaddada bukatar kai ɗauki wa ƙasar Italiya inda nan ne mafi yawan 'yan gudun hijirar ke zuwa. Duk da cewar mutane kalilan ne suka cimma isowar nahiyar turai da ɓarkewar boren na Libya, hukumomin turan sun fara bayyana damuwa dangane da yawan 'yan gudun hijira da ke fitowa daga yankin arewacin Afrika. Guido Westerwelle ministan harkokin wajen tarayyar Jamus ya na mai cewar " kamar yadda ba bu abunda za mu iya yi, kuma bama son yadda 'yan yankin arewacin Afrika ke cigaba da kwarara zuwa Turai, mu na da muradin ganin cewar an cimma warware rigingimun siyasar yankin, kuma komai ya daidaita. Amma tabbatar da democradiyya na nufin sauyi, ta yadda mutane za su zauna acikin kasashensu".
Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Abdullahi Tanko Bala