Ƙarshen yaƙin neman zaɓe a Nijar
March 10, 2011A Jamhuriyar Nijar an rufe yaƙin neman zaɓe zagaye na biyu, bayan kwanaki 14 ana fafatawa tsakanin yan takara guda biyu, wato Mahamadu Isufu na jam´iyar PNDS Tarayya da Seini Umaru na MNSD-Nasara.
A jimilce za a iya cewar a wannan karo ma, jamhuriya Nijar ta zama abin koyi a nahiyar Afrika, ta fannin demokraɗiya, ta la´akari da yadda wannan yaƙin neman zaɓe ya wakana lami lafiya, ba tare da samun wani hargitsi ko tashin hankali ba, duk kuwa da daddagewar da ɓangarorin biyu su ka yi na yayata manufofinsu ga al´umar ƙasa, da kuma yadda yaƙin neman zaɓen ya haddasa rabuwar kanu tsakanin jam´iyu.
Illa Kane shine shugaban ƙungiyar yan jarida ta Nijar, ya bi sau da ƙafa wannan yaƙin neman zaɓe, ya kuma yi tsokaci game da dallilan da su ka sa yakin neman zaɓe a Nijar saɓanin wasu ƙasashen Afrika ke gudana cikin kwanciyar hankali.
'Yan takara biyu sun shirya tarruruka a sassa dabandaban na ƙasa, inda su ka bayyana manufofinsu ga al´uma,kuma kowa ya buƙaci jama´a ta bashi haɗin kai.
Tun lokacin da saban iskan demokraɗiya ya kaɗa a Jamhuriya Nijar a farkon shekara 1990, wannan shine karo na biyar a na shirya zaɓen shugaban ƙasa, kuma so ukku kenan ana karon ƙarshe tsakanin jam´iyun MNSD-Nasara da PNDS Tarayya.
A zaɓɓuɓuka biyu na baya, ɗan takara MNSD-Nasara wato tsofan shugaban ƙasa, Tanja Mamadu ke samun galaba a yayi da Mahamadu Isifu abokin hammayarsa ke rungumar kaddara.
Shin a wannan karo ko alamun ɗan takara da ya sha ƙasa zai amince ya rungumu ƙaddara, kamar yadda ta wakana asauran zaɓɓuɓukan da su ka wuce, Illa Kane ya yi tokaci akai.
A halin yanzu dai kura yaƙin neman zaɓe ta kwanta, hankula kuma sun daɗa karkata wajen hukumar zaɓe mai zaman kanta, wadda ta ce ta tanadi komai domin shirya zaɓe lami lafiya ranar gobe idan Allah ya kai mu. Tare da fatan Allah shi ba mai rabo sa´a.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Mohammad Nasiru Awal